Kalli yawan kudaden da suke ajiye a Najeriya wanda har yanzu kotu bata bada damar a taba su ba

Kalli yawan kudaden da suke ajiye a Najeriya wanda har yanzu kotu bata bada damar a taba su ba

Fiye da rabin tiriliyan na nairori ke kulle a sassa daban daban na wadanda suka aikata cin hanci da rashawa, wadanda a yanzu haka suke jiran kotu ta kammala shari'a a kansu domin amfani dasu

Kalli yawan kudaden da suke ajiye a Najeriya wanda har yanzu kotu bata bada damar a taba su ba

Kalli yawan kudaden da suke ajiye a Najeriya wanda har yanzu kotu bata bada damar a taba su ba

Fiye da rabin tiriliyan na nairori ke kulle a sassa daban daban na wadanda suka aikata cin hanci da rashawa, wadanda a yanzu haka suke jiran kotu ta kammala shari'a a kansu domin amfani dasu, inji Gwamnatin Najeriya.

Ministan yada labarai, Lai Mohammed yace anyi hakan ne domin kare doka ta shida ta zababbu da shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu.

DUBA WANNAN: Wata mata ta gwammace bara maimakon nemawa diyarta lafiya

"Wannan dokar zata shafi laifuffuka cin hanci da rashawa 155 dake gaban kuliya. Jimillar kudin da ake sa ran fitar su sun kai rabin tiriliyan," inji Mohammed.

"Wannan kudaden suna da yawa, yafi Naira biliyan 500 da aka fitar karkashin gwamnatin nan don shirin hannun jari na kasafin kudin 2018 da kuma Naira biliyan 344 da aka ware don gyara da aikin tituna na fadin kasar nan a kasafin kudin 2018."

Gwamnatin tace dokar tana takaita mu'amala ne da kadarorin da ake zargin an same su ta rashawa kuma ana bincike akan su. Gwamnatin tace duk wanda ake zargi ba zai samu damar amfani da kudin shi ba don yin magudi a kotu.

Masu kalubalanta sunce dokar ta sabawa kundin tsarin mulki kuma karantsaye ce ga Sharia.

Mohammed ya jajirce gurin ganin ansa hannu domin tabbatar wa da mutane cewa yaki da rashawa da Buhari yake yi, ba da wasa yake ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel