Ana cigaba da nuna yatsa tsakanin APC da PDP a kan zaben Ekiti

Ana cigaba da nuna yatsa tsakanin APC da PDP a kan zaben Ekiti

- Sakataren yadda labaran kasa na PDP, Ologbondiyan, yace jam'iyyarsa bata amince da sakamakon zaben Ekiti ba saboda an tafka magudi

- Ologbondiyan yace gwamnonin wasu jihohin musamman wanda ke makwabtaka da Ekiti sun iso jihar inda suka taimaka wajen tattaro mutanen da zasu sayo kuri'ar mutane

- Sai dai wani mamaban APC, Sanata Ayo Arise yace ya yi watsi da zargin inda yace jam'iyyarsa bata bi mutane tana sayar kuri'unsu kamar yadda ake sayar da kaya a shago ba

An tafka mahawara a gidan talabijin na Channels a shirin Sunrise Daily ta ranar Talata, 17 ga watan Yuli yayin da jami'iyyar APC da na PDP suka rika musayar maganganu game da zaben gwamna da aka kammala a Ekiti.

Sakataren yadda labaran kasa na PDP, Kola Ologbondiyan, yace jam'iyyarsa bata amince da sakamakon zaben Ekiti ba saboda an tafka magudi.

Ana cigaba da nuna yatsa tsakanin APC da PDP a kan zaben Ekiti

Ana cigaba da nuna yatsa tsakanin APC da PDP a kan zaben Ekiti

DUBA WANNAN: 'Yan majalisar Ekiti sun yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar

Ologbondiyan yace: "Gwamnonin wasu jihohin musamman wanda ke makwabtaka da Ekiti sun iso jihar inda suka taimaka wajen tattaro mutanen da zasu sayo kuri'ar mutane.

"Abinda ya faru a Ekiti fashi da makami ne da rana tsaka. Hakan yasa jam'iyyar mu taki amincewa da sakamakon zaben baki daya. Abinda ya faru tsabar damfara ce kawai," inji shi.

Sai dai wani mamaban APC, Sanata Ayo Arise yace ya yi watsi da zargin inda yace jam'iyyarsa bata bi mutane tana sayar kuri'unsu kamar yadda ake sayar da kaya a shago ba

Yace: "Jam'iyyar PDP ce ta fara sayan kuri'un mutane tun kwanaki biyu gabanin zaben, suna ta aika wa mutane da kudade. Sun aika wa dukkan masu jefa kuri'a da kudi.

"An zo an fada mana cewa jami'an jami'iyyar PDP sun gama saye kuri'in mutane. Sai muka ce idan har PDP tana sayan kuri'in mutane, yanzu mutane zasu fara tambayar mu kudi.

"A tunani na abinda ya faru a Ekiti yana daya daga cikin manyan matsalolin da ke adabar Najeriya kuma dole mu nemi mafita saboda babu yadda za'ayi wani ya fara sayan kuri'un mutane kuma ya yi tsamanin zan zuba idanu ina kalonsa."

A kan batun na'urar tantance masu kada kuri'a, Kakakin PDP yayi zargin cewa INEC ta samarwa kananan hukumomin da APC suke da rinjaye na'ura masu kyau amma ba bawa wuraren da PDP ke da rinjaye na'ura marasa kyau.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel