Kaico! Wani Matashi ya daddatsa Mahaifiyarsa gunduwa gunduwa

Kaico! Wani Matashi ya daddatsa Mahaifiyarsa gunduwa gunduwa

Ke duniya, ina zaki damu ne!! a yayin da duk wani Dan halas, kuma Da na kirki ke iya bakin kokarinsa na ganin ya faranta ma iyayensa rai ta hanyar binsu sau da kafa da girmamawa, tare da fatan ganin ya rabu dasu lafiya, wasu kuma kuntata ma nasu iyayen suke yi.

A nan, runduna Yansandan jihar Osun ne ta kama wani Matashi a kauyen Ogunjija, a ranar Talata, 17 ga watan Yuli, mai suna Sifau Michael mai shekaru Arba’in bayan ya yi amfani da adda ya halaka Uwarsa mai suna Auwalatu Sifau, mai shekaru sittin.

KU KARANTA: Rashin Imani: Wani Mutumiya kashe wani Yaro kwanaki biyu da sakin mahaifiyarsa

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito da Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Folashade Odoro tana cewa da misalin karfe 2:30 na ranar Litinin aka kawo musu rahoton kisan.

Kaakakin ta shaida ma majiyar Legit.ng cewar wani mazaunin Unguwar mai suna Segun Atanda ne ya tsegumta ma jami’an Yansana cewa SIfau ya kashe mahafiyarta ta hanyar daddatsata gunduwa gunduwa da adda.

Sai dai majiyar Kaakakin bata bayyana dalilin da yasa Yaron ya kashe mahaifiyartasa ba, amma ta bayyana cewa Yansanda sun kaddamar da bincike game da lamarin, kuma da zarar sun kammala gudanar da binciken zasu gabatar da shi a gaban kuliya manta sabo.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel