Rana zafi inuwa kuna: Gwamnati ta yi ma gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose daurin talala

Rana zafi inuwa kuna: Gwamnati ta yi ma gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose daurin talala

Dan uwan gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, Isaac Fayose ya bayyana mawuyacin halin da gwamnan ya shiga tun bayan sanar da sakamakon zaben gwamna jihar Ekiti, wanda dan takarar jam’iyyar APC, kuma tsohon gwamnan jihar,Kayode Fayemi ya lashe.

Isaac yace akalla jami’an Yansanda dubu daya ne aka girke, wanda suka yi ma fadar gwamnatin jihar Ekiti kawanya, domin hana gwamnan fita daga gidansa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

KU KARANTA: Ta leko ta koma: Gwamnan jihar Ebonyi ya karyata batun komawarsa APC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Isaac ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda yace: “A yanzu haka gwamnati ta rufe layukan wayan gwamna Ayodele Fayose, sa’annan Yansanda dubu daya sun zagaye gidan gwamnati.

Rana zafi inuwa kuna: Gwamnati ta yi ma gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose daurin talala

Yansanda a gab Gwamnati

“Babu wanda zai iya fita daga gidan, sun mana daurin talala, muna fargabar abinda zai iya faruwa ga rayuwarmu, da rayuwar gwamnan kansa, don kuwa suna shirin kashe shi ne. kuma sun rufe dukkanin tashoshin rediyo da na Talabijin dake jihar.” Inji shi.

Daga karshe Isaac ya bukaci jama’a da su cigaba da watsa wannan bayani har sai an samu wanda zasu kai musu agaji, “Muna cikin hadari, kada ku bari a kashe Fayose.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel