'Yan majalisar Ekiti sun yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar

'Yan majalisar Ekiti sun yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar

Majalisar jihar Ekiti ta dage duk wata zaman majalisar har sai ranar 8 ga watan Oktoban shekarar 2018 saboda barazana ga lafiyarsu da rayyukarsu da ake yi.

Majalisar tace zata cigaba da zamanta ne lokacin da wa'addin mulkin gwamnan mai ci, Ayodele Fayose ta zo karshe.

Har ila yau, majalisar tayi watsi da sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar da ya gabata wanda tsohon gwamnan Kayode Fayemi na jam'iyyar APC ya yi nasara.

'Yan majalisar Ekiti sun yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar

'Yan majalisar Ekiti sun yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar

Galibin mambobin majalisar dai mabiya goyon gwamna Ayodele Fayose na jam'iyyar PDP ne.

DUBA WANNAN: Yadda daga addu'a wani dan tsibu ya zake wa wata daliba

Shugaban majalisar, Akinyele Olatunji, ya bayyana cewa yadda aka gudanar da zaben da kuma sakamakon zaben a matsyain abin takaici.

Mr Akinyele, ya yi Allah wadai da irin cin mutuncin jami'an tsaro suka da yiwa gwamna Ayodele Fayose, da shugabanin jam'iyyar APC da kuma sauran mambobin majalisar jihar.

Mr Akinyele, yace dole ne su tafi wannnan hutun mai tsawo saboda irin barazana da cin mutunci da jami'an tsaro keyi musu saboda dalilan siyasa.

A yayin da yake magana, Ciyaman din kwamitin sadarwa na majalisar jihar, Samuel Omotoso ya ce zaben da aka gudanar a ranar 14 ga watan Yuli bai cika sharrudan demkradiyya ba.

A cewarsa, anyi ta siyan kuri'un jama'a da kuma tayar da hankula har ma da kirkirar sakamakon karya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel