Yan sanda sun kama mutane 5 dake yada jabun dala

Yan sanda sun kama mutane 5 dake yada jabun dala

Kwamishinan yan sanda a jihar Gombe, Shina Olukolu a ranar Talata, 17 ga watan Yuli ya bayyana cewa yan sanda sun kama wasu mutane biyar dake dauke da jabun daloli a Gombe, babban birnin jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Olukolu ya bayyana a wata sanarwa ga manema labarai a Gombe cewa an kama su dauke da dala 100 na Amurka guda 60.

Ya bayyana cewa wadanda aka kama sun yi amfni da damar aikin hakki da Musulmai ke shirin tafiya kasar Amurka wajen damfarar mahajattan da basu sani bat a hanyar sayar masu da jabun daloli.

Yan sanda sun kama mutane 5 dake yada jabun dala

Yan sanda sun kama mutane 5 dake yada jabun dala
Source: Depositphotos

Kwamishinan ya shawarci mahajjata das u guje ma siyan daloli daga wadanda ba’a yarje mawa ba da wuraren dake basu kudin kan farashi mai ban mamaki.

KU KARANTA KUMA: Za’a kashe N242.4bn a zaben 2019 – Buhari ga majalisar dokoki

Ya bayar da tabbacin cewa yan sanda za su ci gaba da bibiyar shirin yan damfara, ta kama su sannan ta hukuntasu daidai da doka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel