Ayi hattara: fashewar tukunyar Gas ta kashe yara 3, biyu sun jikka a Jigawa

Ayi hattara: fashewar tukunyar Gas ta kashe yara 3, biyu sun jikka a Jigawa

- Wani mummunan tsautsayi ya afku a jihar jigawa

- Har ta kai ga asarar rayukan yara 3 yayin da wasu suka raunata

- A sakamakon bindigar da tukunyar Gas tayi

A kalla kimanin yara guda 3 ne su ka rasa ransu a kauyen Sara da ke karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa, biyo bayan fashewar da tukunyar gas ta yi.

Ayi hattara: fashewar tukunyar Gas ta kashe yara 3, biyu sun jikka a Jigawa

Ayi hattara: fashewar tukunyar Gas ta kashe yara 3, biyu sun jikka a Jigawa

Kakakin rundunar yan sanda na jihar Jigawa ASP Abdu Jinjiri ne ya tabbatar da faruwar lamarin tare kuma da bayyana wadanda su ka jikkata.

"A makon da ya gabata ne aka samu fashewar tukunyar gas a gidan Alhaji Wada Sara, wanda ya haddasa samun raunika ga iyalinsa. Jim kadan da faruwar wannan mummunan al'amari, sai aka garzaya da su zuwa cibiyar lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Birnin Kudu, domin duba lafiyarsu" in ji Abdu Jinjiri.

KU KARANTA: Manyan abubuwa guda 8 dake kawo mutuwar aure daga bangaren Miji

Ya kara da cewa "Fatima mai shekaru 3 da Zainab mai shekaru 2 da kuma Abdulrahman dan kimanin shekaru 4 duk sun rasa ransu ne a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano".

A karshe yayi kira ga al'umma da su kara lura sosai a lokacin da su ke amfani da tukunyar gas din domin girki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel