Barawon da ya tsare daga wurin ‘yan sada ya sake shiga hannu

Barawon da ya tsare daga wurin ‘yan sada ya sake shiga hannu

- Mara gaskiya ko a ruwa gumi yake in ji masu iya magana

- Bayan aikata laifin sata da sulalewa daga hannun 'yan sanda an sake damke shi

- Har ma tuni 'yan sanda sun dangana da shi zuwa wurin alkali

An gabatar da wani matashi mai suna Gerald Ogwu dan kimanin shekaru 22 a duniya, wanda ake zarginsa da sace kudi kimanin Naira 75,000 sannan kuma ya tsere daga hannun jami'an yan sanda, a gaban kotun majistire dake Yaba a jihar Lagos.

Karshen alewa kasa: Barawon da ya tsare daga wurin ‘yan sada ya raina kansa a gaban kotu

Karshen alewa kasa: Barawon da ya tsare daga wurin ‘yan sada ya raina kansa a gaban kotu

Ana dai tuhumar Ogwu da laifuffuka guda biyu wadanda suka hada da sata da kuma tsarewa daga hannun yan sanda.

Dan Sanda mai gabatar da kara ASP Nuruddeen Thomas ya shaidawa kotun cewa Ogwu ya aikata laifin ne a ranar 16 ga watan Yuni akan titin Ilaje da ke unguwar Bariga.

KU KARANTA: Baku san aikinku ba: Buhari ya watsa ma yan majalisu kasa a ido akan wasu bukatu 4 da suka mika masa

Thomas ya kara da cewa wanda ake zargin, ya sace kudi kimanin Naira 75,000 tare da wayar tafi da gidanka kirar kamfanin itel mallakin wani ma'aikacin gidan ruwa na Ozone. Sannan kuma ya tsere daga hannun jami'an yan sanda a lokacin da ake tsaka da bincike.

Wanda hakan ya saba da sashe na 106 (b) da kuma sashe 287 na kundin manyan laifuffukan na jihar Lagos.

A karshe Babban alkalin kotun majistiren Mista Kike Ayeye ya bayar da belin wanda ake zargin akan kudi Naira 100,000 tare kuma da kawo wanda zai tsaya masa.

Daga nan ne mai shari’ar ya dage sauraron shari'ar har sai ranar 16 ga watan Agusta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel