Ta leko ta koma: Gwamnan jihar Ebonyi ya karyata batun komawarsa APC

Ta leko ta koma: Gwamnan jihar Ebonyi ya karyata batun komawarsa APC

Gwamnan jihar Ebonyi,David Umahi ya musanta rahoton dake yawo a shafukan yanar gizo na cewa wai ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP, inda yace babu kamshin gaskiya a cikin wannan batu, labari ne kawai na kanzon kurege.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Umahi ya bayyana haka ne a fadar gwamnatin jihar Ebonyi dake Abakaliki a ranar Talata, 17 ga watan Yuli, inda yace duk da cewa akwa kyakkyawar alaka tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, amma bai koma APC ba.

KU KARANTA: Baku san aikinku ba: Buhari ya watsa ma yan majalisu kasa a ido akan wasu bukatu 4 da suka mika masa

“Akwai kyakkyawar danagantaka tsakanina da shugaba Buhari, kuma Maigidana ne, kuma bai taba gayyatata na shiga jam’iyyar APC ba, kuma babu wanda ya taba min wannan gayyatar, bugu da kari babu wani dalili da zai sanya ni ficewa daga PDP.

Ta leko ta koma: Gwamnan jihar Ebonyi ya karyata batun komawarsa APC

David Umahi
Source: Depositphotos

“PDP ta yi min riga ta yi min wando, ta yi min komai, na taba zama shugaban PDP a jaha, kuma na zama mataimakin gwamna, yanzu nake gwamna duk a inuwar jam’iyyar PDP, kuma ni tsayayyen mutum ne, duk wanda aka ga yana sauya jam’iyya ba tsayayye bane, sai dai idan akwai matsala a jam’iyyar.

“Don haka daga yau, har zuwa goba, kai har duniya ta nade, b azan fice daga PDP ba, idan ma ta kai ga sai na fita daga PDP, tabbas b azan shiga jam’iyyar APC ba, musamman irin APC ta jihar Ebonyi, saboda shuwagabanninta a jihar nan sun karya mana jaha.” Inji shi.

Daga karshe ya gargadi duk masu yada wannan rahoto da nufin su kawo matsala a siyasar jihar Ebonyi su daina, don kuwa babu abin dake gabansa da ya wuce ya janyo ma jihar Ebonyi ayyukan cigaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel