Ya kamata Buhari, Tinubu da sauransu su saita kansu – Satguru Maharaji

Ya kamata Buhari, Tinubu da sauransu su saita kansu – Satguru Maharaji

Satguru Maharaji ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bola Tinubu da sauran mutane su yiwa kansu fada sannan su nemo mafita ga kashe-kashen makiyaya a kasar.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a kauyen Maharaji dake jihar Lagas.

A cewar Satguru wannan matsala na rashin tsaro a kasar ya sabama shugabancin damokradiyya.

Sannan kuma ya bukaci yan Najeriya da su tuhumi shugabanninsu saboda hakkin gwamnati ne samar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummanta.

Ya kamata Buhari, Tinubu da sauransu su saita kansu – Satguru Maharaji

Ya kamata Buhari, Tinubu da sauransu su saita kansu – Satguru Maharaji

Ya kuma bayyana cewa an kwato biliyoyin naira a yaki da cin hanci da rashawa amma babu wani abun nunawa kamar dai yan kwallon “Super Eagles.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON, da wasu mutane 13 a FCSC

Ya kuma roki shugabannin das u ba matasa damar shiga siyasa, cewa muna bukatar sabbin jini.

Da yake nuna goton bayansa ga Buhari, Satguru ya bukaci yan Najeriya da su ba shugaban kasa Muhammadu Buhari goyon baya, sannan su nuna mai hanya a duk inda yayi kuskure.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel