Za’a kashe N242.4bn a zaben 2019 – Buhari ga majalisar dokoki

Za’a kashe N242.4bn a zaben 2019 – Buhari ga majalisar dokoki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da majalisar dokokin kasar cewa za’a kashe naira biliyan 242.4 a zaben 2019.

Shugaban kasar ya bayyana akan a wata wasika da aike ga majalisar dattawa a ranar Talata, 17 ga watan Yuli wanda aka karanta a zangon majalisa.

Ya yi bayanin cewa amincewa da kasafin Naira triliyan 9.12 a 2018 zai zamo kalubale don haka bai bad a shawaran kara kasafin kudin 2018 ba domin samun damar ware kudaden da ake bukata domin zaben 2019.

Za’a kashe N242.4bn a zaben 2019 – Buhari ga majalisar dokoki

Za’a kashe N242.4bn a zaben 2019 – Buhari ga majalisar dokoki

Don haka ya bukaci majalisar dokokin kasar da ta tura kudaden ga inda ya kamata don sabbin ayyukanda aka kasar a kasafin kudin 2018 domin samun naira biiyan 228.8 na zabe.

KU KARANTA KUMA: 2019: PDP na zawarcin Saraki da Lai Mohammed

Shugaban kasar ya bayyana cewa ragowar kudin zai kasance a kasafin kudin 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel