Gwamnatin kano zata kashe fiye da miliyan N27m domin sayen kwanukan awo(mudu) domin rabawa ‘yan kasuwa

Gwamnatin kano zata kashe fiye da miliyan N27m domin sayen kwanukan awo(mudu) domin rabawa ‘yan kasuwa

- Gwamnatin Kano zata kashe sama da Naira miliyan N27m domin sayen kwanukan awo, da aka fi sani da mudu, domin rabawa masu awo a kasuwannin jihar

- Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, ya bayyana hakan ne a jiya, Litinin, bayan kamala taron majalisar zartarwa na jihar ta kano

- Garba ya kara da cewar gwamnatin jihar ta Kano zata kasha wasu kudaden, Naira miliyan N253m domin samar da magudanun ruwa da zasu magance matsalar zaizayar kasa

Gwamnatin Kano, ta bakin kwamishinanta na yada labarai, Malam Muhammad Garba, ta bayyana cewar zata kasha sama da Naira miliyan N27m domin sayen kwanukan awo, da aka fi sani da mudu, domin rabawa masu awo a kasuwannin jihar.

Gwamnatin kano zata kashe fiye da miliyan N27m domin sayen kwanukan awo(mudu) domin rabawa ‘yan kasuwa

Gwamnan Kano, Ganduje

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a jiya, Litinin, bayan kamala taron majalisar zartarwa na jihar ta kano. Kazalika ya bayyana cewar gwamnatin Kano zata kasha fiye da Naira miliyan N400m don gudanar da wasu aiyuka a bangaren kiwon lafiya.

DUBA WANNAN: Bayan kammala zaben Ekiti, Obasanjo ya sake rangada wata zungureriyar wasikar

Garba ya kara da cewar gwamnatin jihar ta Kano zata kasha wasu kudaden, Naira miliyan N253m domin samar da magudanun ruwa da zasu magance matsalar zaizayar kasa a Zangon Marikita dake karamar hukmar Ungogo da kuma Garo a karamar hukumar Garo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel