Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON, da wasu mutane 13 a FCSC

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON, da wasu mutane 13 a FCSC

A ranar Talata, 17 ga watan Yuli, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya nadawani tsohon mai ba jam’iyya mai mulki, APC shawara akan doka, Muiz Banire a matsayin shugabanhukumar kula da kadarori na Najeriya.

Shugaba Buhari ya nada Banire wadda ya kasance babban lauyan Najeriya a rana Talata 17 ga watan Yuli.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban kasar ya kuma nada kwamishinoni 12 a hukuma ma’aikatan gwamnatin tarayya (FCSC).

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya nada Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON, da wasu mutane 13 a FCSC

Shugaba Buhari ya nada Muiz Banire a matsayin shugaban AMCON

KU KARATA KUMA: Babu shaidar da ya nuna cewa anyi magudin zabe a Ekiti - CDD

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya karanta wasikan shugaban kasar a gaban majalisa wadda a ciki ya nemi yardan majalisar.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Cibiyar ci gaban damokradiya (CDD), a ranar Lahadi ya bayyana cewa zuwa yanzu babu wani shaida dake nuna cewa anyi magudin sakamakon zaben gwamna da aka yi a ranar Asabar a jihar Ekiti.

Manema labarai sun rahoto cewa CDD na daga cikin kungiyar jama’a a fadin kasar da hukumar zabe mai zaman kanta ta tattance domin lura da zaben Ekiti wanda aka gudanar a ranar 14 ga watan Yuli.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel