Jihar Kebbi na samar da Tan 3.6m cikin Tan 5.7m na Shinkafa da Najeriya ke bukata a duk shekara

Jihar Kebbi na samar da Tan 3.6m cikin Tan 5.7m na Shinkafa da Najeriya ke bukata a duk shekara

Da sanadin shafin jaridar nan ta Daily Nigerian mun samu rahoton cewa, jihar Kebbi ce zakaran gwajin dafi sakamakon kasancewar ta kan gaba tare da cirar tuta wajen yiwa kasar nan ta Najeriya hidima ta samar da shinkafa da kasar take bukata cikin kowace shekara.

Muhammad Shehu, sakataren dindindin na ma'aikatar noma ta jihar Kebbi, shine ya bayyana hakan da cewar jihar ta na samar da tan miliyan 3.6 cikin tan miliyan 5.7 na shinkafa da kasar nan take bukata a duk shekara.

Legit.ng ta fahimci cewa, Mista Shehu ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai na NAN a Birnin Kebbi a ranar Talatar da ta gabata.

Yake cewa, jihar Kebbi ke samar da tan miliyan 3.6 na shinkafa cikin tan miliyan 5.7 na abinci da ake bukata a fadin kasar nan cikin kowace shekara, inda ya ce wannan dalili ne ya sanya jihar take kan gaba tare da yiwa sauran jihohi fintikau ta fuskar samar da shinkafa a kasar nan.

Jihar Kebbi na samar da Tan 3.6m cikin Tan 5.7m da Najeriya ke bukata a duk shekara

Jihar Kebbi na samar da Tan 3.6m cikin Tan 5.7m da Najeriya ke bukata a duk shekara

Ya ci gaba da cewa, wannan mataki da jihar ta kai a halin yanzu ya zo ne a sanadiyar kokari da jajircewar sama da kaso 70 cikin 100 na matasa da kuma mata dake amfanuwa da shirin nan na shinkafa da gwamnatin jihar ta tanadar.

KARANTA KUMA: Rayuka 38, Gidaje 200 sun salwanta cikin wata Ambaliyar Ruwa a jihar Katsina

Babban sakataren ya kara da cewa, samar da shinkafa ya taka rawar gani tare da tasiri wajen inganta matsayin manoma tare da habaka zamantakewa da amincin kananan manoma da a halin yanzu tuni sun yi hannun riga da talauci.

Ya kuma yabawa kokarin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Atiku Bagudu, dangane da tabbatar da farfadowar harkokin noma ta hanyoyi na shirye-shirye daban-daban ga manoma a fadin jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel