EFCC ta sake kama tsohon gwamna Orji Kalu, ta kara adadin tuhumar da ake masa

EFCC ta sake kama tsohon gwamna Orji Kalu, ta kara adadin tuhumar da ake masa

A yau Talata ne aka sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu, a gaban wata kotun tarayya dake Lagos bisa tuhumarsa da aikata laifuka 39 masu alaka da zamba cikin aminci.

Hukumar yaki da masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC ne ta maka tsohon gwamnan wanda a halin yanzu ya dawo jam'iyyar APC dake mulkin kasa.

Hukumar ta EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan ne tare da tsohon kwamishinan kudi, Ude Udeogo da kuma wata kamfani mai suna Slok Nigeria Ltd wanda ake ce mallakar Mr. Kalu ne.

EFCC ta sake kama tsohon gwamna Orji Kalu, ta kara adadin tuhumarsa da ake masa

EFCC ta sake kama tsohon gwamna Orji Kalu, ta kara adadin tuhumarsa da ake masa

DUBA WANNAN: Yadda daga addu'a wani dan tsibu ya zake wa wata daliba

A ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2016, hukumar ta EFCC ta shigar da kara tuhumar aikata laifuka 34 ciki har da zambar N3.2 biliyan.

Sai dai a lokacin Mr Kalu da Mr Udeogo sun musanta zargin aikata laifin kuma kotu ta bayar da belinsu.

Hukumar EFCC ta kule sauraron karar a watan Mayun 2018 bayan ta gabatar d shaidu 18 da kuma gabatar da hujoji masu dimbin yawa a gaban kotun.

Ana tuhumar Mr. Kalu da wani Emeka Abone da Micheal Akpan ta hada baki wajen karkatar da kudi N7.2 biliyan daga asusun jihar Abia tsakanin Satumban 2001 zuwa Satumban 2006.

Laifin da ya ci karo da sashi na 14, 16(6), 16, 17 da 21 na dokar haramta karkatar da kudade na 2005

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel