Jam’iyyar PDP ce ta yi watsi da aikin jirgin kasan Abuja, gwamnatin mu kuma ta karasa – In ji Osinbajo

Jam’iyyar PDP ce ta yi watsi da aikin jirgin kasan Abuja, gwamnatin mu kuma ta karasa – In ji Osinbajo

- Bayan cecekucen rinton aikin da aka zargi APC da shi dangane da aikin jirgin kasan Abuja, Osinbajo yayi karin haske

- Mataimakin shugaban kasar ya zayyana yadda gwamnatin da ta gabace su ta rika watsi da aiyuka ba tare da kammalawa ba

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya zargi jamiyyar PDP da yin watsi da aikin titin jirgin kasan Abuja.

Jam’iyyar PDP ce ta yi watsi da aikin jirgin kasan Abuja, gwamnatin mu kuma ta karasa – In ji Osinbajo

Jam’iyyar PDP ce ta yi watsi da aikin jirgin kasan Abuja, gwamnatin mu kuma ta karasa – In ji Osinbajo

Idan za'a iya tunawa dai a makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammad Buhari ya kaddamar da jirgin kasan da zai rinka zirga-zirga a birnin tarayyar Abuja, wanda kuma jamiyyar PDP ce ta fara aiwatar da aikin tun asali.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a gurin taron inuwar yan kasuwa wanda fadar shugaban kasa ta shirya.

"Mun yi alkawarin karasa dukkanin wani aiki da mu ka samu ba'a kammala shi ba, to hakika kam gwamnatinmu za ta tabbatar da ganin an karasa shi, domin amfanin al'ummar kasar nan" in ji mataimakin shugaban kasar.

KU KARANTA: Fayose zai gurfana a kotu bayan karewan wa’adinsa - EFCC

Ya kuma bayar da misalin irin gagarumar nasarar da gwamnatinsu ta yi akan yadda su ka kammala aikin titin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Abuja.

"Mu Kalli yadda yadda titin dogo wanda ya taso daga Kaduna zuwa Abuja, an fara shi tun tsawon lokaci amma sai gwamnatinmu ce ta kai ga kammala aikin" in Osibanjo.

A karshe Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa har yanzu gwamnatinsu tana nazari akan sanya hannu na huldar kasuwanci a tsakankanin kasashen afrika, domin ko a wancan makon da ya gabata sai da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya zo kasar nan, inda su ka tattauna kan muhimman batutuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel