Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Yanzu-yanzu: Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya musanta rahoton da ya yadu a kafafan yada labarai cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar People Democratic Party PDP zuwa All Progressives Congress, APC a ranan Talata, 17 ga watan Yuli, 2018.

Legit.ng ta samu rahoto mara tabbas cewa gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.

Wannana na faruwa ne bayan gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana fitarsa daga jam'iyyar APC amma bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba.

Shugbaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole, ya bayyana cewa gwamna Samuel Ortom ba fada musu da kansa ba cewa zai bar jam'iyyar ba.

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya watsawa jam’iyyar APC kasa a ido yayinda ya ki amsa sammacin da shugabancin jam’iyyar tayi masa tare da tsohon uban gidansa, George Akume, a sakatariyar jam’iyyar.

Shi Akume ya masa goron gayyatar inda suka tattauna da mataimakin shugaban jam’iyyar, Sanata Lawal Shaiubu, kan yadda za’a samu mafita daga cikin rikicin da ke tsakaninsu da Ortom.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel