2019: PDP na zawarcin Saraki da Lai Mohammed

2019: PDP na zawarcin Saraki da Lai Mohammed

Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), reshen jihar Kwara sun roki shugaban majalisar dattawa da ministan bayanai, Lai Mohammed da su dawo jam’iyyar adawa.

A wani jawabi dauke das a hannun Abdullahi Lateef, Moshood Issa, Danjumo Hamid, Olabode M. A. da Ayinde Wasiu, kungiyar ta bukaci shugaban gamayyar kungiyar APC, reshen jihar Kwara, Bashir Bolarinwa da su koma PDP, jaridar Punch ta ruwaito.

Legit.ng ta lura cewa kungiyar ta bayyana Saraki, Mohammed da Boalarinwa a matsayin ‘masu canza wasa’ wadda zai iya kawo canji ga albarkatun PDP a 2019.

2019: PDP na zawarcin Saraki da Lai Mohammed

2019: PDP na zawarcin Saraki da Lai Mohammed

Idan za ku tun Legit.ng ta rahoto a baya cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta yi kira ga shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal da Sanata Aliyu Wamakko, tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso da kum tsohon gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje kan su dawo domin su kwace mulki daga hannun jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a shekara mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Babu shaidar da ya nuna cewa anyi magudin zabe a Ekiti - CDD

Wani babban jigon kwamitin masu ruwa da tsaki da jam’iyyar da yayi Magana cikin takawa yace: “Mun fara tattaunawa da Sraki da sauransu. Kamar ma ace muna rokons ne da su dawo tushensu daga cikin kokarin da ake yi na kafa babban manufa a PDP."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel