Yadda wani magidanci ya bi matarsa gidan iyayenta ya kashe ta saboda tayi yaji

Yadda wani magidanci ya bi matarsa gidan iyayenta ya kashe ta saboda tayi yaji

Hukumar Yan sanda reshen jihar Neja ta kama wani Bello Muhe mai shekaru 25 dake zaune a kauyen Gurechi dake karamar hukumar Borgu na jihar bisa tuhumarsa da laifin yiwa matarsa kissar gilla.

Kwamishinan Yan sanda, Mr Dibal Yakadi, ne ya bayar da sanarwar yayin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau Talata a garin Minna.

Yakadi yace wanda ake tuhumar na zaune ne a rugar Fulani dake sabuwar Bussa a kauyen Gurechi dake da iyaka da karamar hukumar Bagudu ta jihar Kebbi.

'Yan sanda sun kama wani magidanci da ya kashe matarsa a Neja

'Yan sanda sun kama wani magidanci da ya kashe matarsa a Neja
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yadda daga addu'a wani dan tsibu ya zake wa wata daliba

Yace wanda ake tuhumar ya samu rashin jituwa da matarasa, Husse Ali, hakan yasa tayi yaji ta koma gidan mahaifinta dake Gurechi.

"Mijin ta bi ta gidan mahaifinta don yin biko amma da ya bukaci su koma tare sai taki amincewa," inji shi.

Kwashinan ya cigaba da cewa, wanda ake tuhumar ya fito da addarsa kuma ya yiwa matar munanan rauni a kai da wuya da kuma bayanta.

Daga nan kuma sai ya gudu zuwa karamar hukumar Bagudu dake jihar Kebbi amma aka bi shi kuma aka kamo shi.

"An garzaya da Husse zuwa asibitin koyarwa na Usmanu Danfodio dake Sakwato don yi mata magani amma ta rasu a asibitin.

Yakadi yace wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa dashi kuma za'a gurfanar dashi gaban kotu bayan an kammala bincike a kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel