Shugaban Kasa Buhari ya lashe zaben 2019 ya gama – Isa Aremu

Shugaban Kasa Buhari ya lashe zaben 2019 ya gama – Isa Aremu

Kwanakin baya mun ji labari cewa wani tsohon Mataimakin Shugaban Hukumar kwadago na kasa watau NLC ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne zai lashe zabe mai zuwa na 2019.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa tsohon Shugaban Kungiyar kwadago na Najeriya Kwamared Issa Aremu ya bayyana cewa Shugaban Kasa Buhari ya ci zaben 2019 ya gaba. Shugaban ‘Yan kwadagon yace wannan a rubuta a ajiye.

Shugaban Kasa Buhari ya lashe zaben 2019 ya gama – Isa Aremu

Tsohon Mataimakin Shugaban NLC na Kasa isa Aremu

Isa Aremu ya tabbarwa Magoya bayan Shugaban Kasa Buhari cewa su sha kurumin su don kuwa Buhari yaci zabe ya gama. Aremu ya bayyana wannan ne lokacin da ake bude ofishin BCO na Kungiyar Magoya bayan Shugaban kasa.

KU KARANTA: Gwamnoni 5 da za su iya fadi zaben 2019

A makon da ya gabata ne Kungiyar Magoya bayan Shugaban Kasa Buhari da ke karkashin lemar “Buhari Campaign Organisation” su ka bude ofishin yakin neman tazarcen Shugaba Buhari a cikin Garin Ilorin da ke Jihar Kwara.

Tsohon Shugaban na NLC ya bayyana cewa Gwamnatin Buhari tana da son Talakawa don haka za ta lashe zaben. Kwamared Aremu ya bayyana yadda Buhari ya biya Gwamnoni kudi domin su biya bashin albashin da ake bin su.

Isa Aremu ya nuna cewa ana sa rai kuma Shugaban Kasa Buhari zai kara albashin Ma’aikata a Kasar. Shugaban Magoya bayan Shugaba Buhari a Jihar Kwara Kwamared Abubakar Al-Hassan Sulaiman yace Buhari zai yi nasara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel