Abin tausayi: Wani dalibin shekarar karshe a jami’a ya fada rijiya bayan da jami’an SARS suka biyo shi (Hotuna)

Abin tausayi: Wani dalibin shekarar karshe a jami’a ya fada rijiya bayan da jami’an SARS suka biyo shi (Hotuna)

- Dalilin karar kwana, wani matashi ya hadu da ajalinsa yayin gujewa kamun 'yan sanda

- Bayan sumamen da 'yan sanda suka kai makwancin daliban ne suka bazama domin neman mafaka

An tsinci gawar wani dalibin shekarar karshe dake jami'ar Ambrose Alli University a yashe a cikin wata tsohuwar rijiya dake Ekpoma a jihar Edo.

An gano gawar dalibin mai suna Saliu Alli Haruna, wanda ya kasance daliban jami'ar ne a cikin wata tsohuwar rijiya kwana 4 da aka daina ganin zirga-zirgarsa bisa dalilin wasan buya da su ke da jami'an rundunar yan sanda masu yaki da manyan laifuka (SARS), su kayi a tsakaninin daliban jami'ar.

Abin tausayi: Wani dalibin shekarar karshe a jami’a ya fada rijiya bayan da jami’an SARS suka biyo shi (Hotuna)

Abin tausayi: Wani dalibin shekarar karshe a jami’a ya fada rijiya bayan da jami’an SARS suka biyo shi (Hotuna)

KU KARANTA: Dalilin da yasa zan goyi bayan Buhari a zaben 2019 Satguru Maharaj Ji

Tun da farko dai wasu rahotanni sun rawaito cewa a ranar Juma'a ne jami'an rundunar yan sandan suka yiwa dakunan kwanan dalibai tsinke, wannan ta sanya dalibin ya tsorata har ta kai ga ya fada cikin rijiya, ba tare da an ankara ba.

Kwana hudu da bacewarsa ne sai ga shi an gano gawarsa a cikin rijiyar da ya fada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel