Wargi ma wuri yake samu: Kalli irin mutanen da hukumar EFCC ta kama a wata 6

Wargi ma wuri yake samu: Kalli irin mutanen da hukumar EFCC ta kama a wata 6

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) tace ta kama masu laifi 142 daga watan Janairu zuwa watan Yulin shekarar nan

Wargi ma wuri yake samu: Kalli irin mutanen da hukumar EFCC ta kama a wata 6

Wargi ma wuri yake samu: Kalli irin mutanen da hukumar EFCC ta kama a wata 6

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) tace ta kama masu laifi 142 daga watan Janairu zuwa watan Yulin shekarar nan.

Shugaban hukumar mai rikon kwarya, Ibrahim Magu shine ya sanar da hakan a wurin wani taro daya halarta wanda aka sanyawa suna "Africa Unite to Defeat Corruption", wanda manyan hukumar na kasa suka halarta a babba ofishin su dake jihar Lagos, a ranar Larabar data gabata.

DUBA WANNAN: Adeosun: Har yanzu hukumar NYSC taki gabatar da wata kwakkwarar shaida

Ya sanar da cewa al'ummar Najeriya kan su zasu shaida irin aikin da hukumar take yi domin kuwa daga watan Janairun wannan shekarar zuwa watan Yuli ta kama masu laifi 142.

A cewar shi, alamu sun nuna cewa hukumar ta dauko hanya na kawo karshen cin hanci da rashawa, koda kuwa ta halin kaka. "Hukumar kuma ta samu nasarar bankado wasu makudan kudade, da dukiyoyi na biliyoyin daloli. Irin wannan cin hancin yayi yawa, kuma baza mu taba amincewa da hakan ba," inji shi.

Ya ce Najeriya tana murnar ranar yaki da cin hanci da rashawa ne saboda tana daya daga cikin kasashen Afrika da suka bada himma wurin kawo karshen shi.

Bayan haka kuma ya bukaci hukumar shari'a ta kasa dasu goya musu baya wurin yaki da cin hanci da rashawan, domin kuwa da sune hakar su zata cimma ruwa.

A karshe Dr Joe Okei-Odumakin tayi kira da hadin kan kowa a kokarin da hukumar take na kawo karshen cin hanci da rashawan, inda take cewa "Dole mu hada karfi da karfe, domin kuwa tafiyar shekaru da dama ana fara ta da taku daya ne, don haka wannan yakin ba wai iya na hukumar nan bane, na kowa da kowa ne."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel