Adeosun: Har yanzu hukumar NYSC taki gabatar da wata kwakkwarar shaida

Adeosun: Har yanzu hukumar NYSC taki gabatar da wata kwakkwarar shaida

- Kwanakin baya ne dai ake zargin cewar ministar kudi Kemi Adeosun ta gabatar da takardar shaidar bautar kasa ta bogi

- Zuwa yanzu dai ana jiran hukumar NYSC ta gabatar da wata shaida, sai dai kuma har yanzu shiru babu amo ba labari

Adeosun: Har yanzu hukumar NYSC taki gabatar da wata kwakkwarar shaida

Adeosun: Har yanzu hukumar NYSC taki gabatar da wata kwakkwarar shaida

Sati daya bayan hukumar masu bautawa kasa ta Najeriya (NYSC) tace ta bada damar gabatar da bincike akan takardar shaidar kammala bautar kasar ministar kudi, Mrs Kemi Adeosun, har yanzu dai hukumar bata kara cewa komai akan maganar inda aka sa gaba ba.

DUBA WANNAN: 2019: APGA ta bukaci Shugaba Buhari ya rattaba hannu a wata doka

A wata sanarwa da hukmar ta fitar satin daya gabata tace ministar ta rubuta takarda akan a bata takardar shaidar kammala bautar kasar, amma har yanzu dai hukumar tana bincike idan har an bata takardar shaidar.

Wani babba a hukumar ta NYSC ya fadawa manema labarai jiya cewar hukumar bazata bayyanawa duniya sakamakon binciken da tayi ba cikin gaggawa, inda yake cewa "A gaskiyar magana babu wata takardar shaida da aka fitar daga wurin mu, amma duk da haka baza suyi magana ba."

Tsohon shugaban hukumar na kasa, wanda a lokacin shine aka fitar da takardar shaidar kammalawan tata, Maharazu Tsiga ya bayyana manema labarai cewa dama hukumar bata amince da bukatar ministar ba na karbar takardar kammalawan ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel