2019: APGA ta bukaci Shugaba Buhari ya rattaba hannu a wata doka

2019: APGA ta bukaci Shugaba Buhari ya rattaba hannu a wata doka

Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi gaggawar rattaba hannu akan dokar shekarar 2010 dake nuni da kyautata tsarin zabe

2019: APGA ta bukaci Shugaba Buhari ya rattaba hannu a wata doka

2019: APGA ta bukaci Shugaba Buhari ya rattaba hannu a wata doka

Jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi gaggawar rattaba hannu akan dokar shekarar 2010 dake nuni da kyautata tsarin zabe, domin bawa jam'iyyu damar fara shirye - shiryen babban zabe mai gabatowa.

DUBA WANNAN: 2019: Atiku ya nemi goyon bayan gwamna Dankwambo na Gwambe

Shugaban jam'iyyar na kasa Dr. Victor Ike Oye, shine yayi wannan kiran jiya a Abuja, a lokacin da yake magana da manema labarai, inda yake jaddada cewar lokaci ya riga ya jima da kurewa a harkokin zaben shekarar 2019.

Oye wanda ya nuns goyon bayan shi akan irin ayyukan da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake na kawo cigaba ga al'ummar kasar nan, ya kuma bukaci 'yan Najeriya dasu zauna lafiya da juna, su kuma bi doka sau da kafa, inda ya kara da cewa Najeriya ita ce kasa daya tak da ta yarda kowanne mutum ya zauna a cikin ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel