Dan sanda ya karbi N100,000 karfi da yaji daga hannun wani

Dan sanda ya karbi N100,000 karfi da yaji daga hannun wani

An tuhumci wasu jami’an yan sanda a jihar Edo da laifin kwatan kudi N100,000 daga hannun wani dan kwangila mai suna, Emmanuel Alabede, ba gaira ba dalili.

Yan sandan sun karbi kudin wannan mutumin ne ta hanyar amfani da na’urar POS bayan sun yi barazanar kasheshi idan ya hanasu.

Jaridar Punch ta samu labarin cewa Emmanuel na hanyan tafiya daga Ibadan zuwa Abuja ne inda yan sandan suka tare motar da yake ciki a titin Ibilo-Okene kuma suka binciki jakunkunan fasinjojin motar.

Dan sanda ya karbi N100,000 karfi da yaji daga hannun wani

Dan sanda ya karbi N100,000 karfi da yaji daga hannun wani

Alabede yace sun bukaceshi ya bayar da wayarsa amma ya ki, sai sukayi barazanar kasheshi idan ya yi taurin kai.

Yace: “Sun duba wayana amma basu ga komai na laifi ba; abinda suka gani shine hotunan gidaje. Sai suka tambayeni ko gidajena ne kuma nace musu ba nawa bane, na wadanda nakewa aiki ne.”

“Sai sukace karya nake, ni dan damfarar yanar gizo ne. sai na musanta hakan kuma na nuna musu katin wajen aiki na,amma duk da haka suka ki sake ni.”

“Yayinda suke rike da wayana, sai aka turo min kudi N200,000. Ganin haka suka ce sai na basu N200,000.”

“Na fada musu ba kudi na bane; na wadanda nakewa aiki ne amma sukace idan ban basu ba, za su kasheni kuma babu abinda zai faru.”

Da ya tsaya kan bakarsa, sai suka cewa direban motan ya tafi. Daga baya dai suka amsa kudi N100,000.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel