Kissar gilla: An garkame saurayin diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo a kurkuku

Kissar gilla: An garkame saurayin diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo a kurkuku

Hukumar Yan sandan Najeriya reshen jihar Ondo ta gurfanar da Alao Adeyemi a gaban kotun Majistare dake Akure, babban birnin jihar Ondo.

An gurfanar da Adeyemi ne bisa zarginsa da kashe Khadijat, diyar mataimakin tsohon gwamnan jihar Ondo, Alhaji Lasisi Oluboyo.

Khadijat, daliba ce a jami'ar Adekunle Ajasin dake Akungba Akoko dake sashin nazarin kula da ilimi dake aji na karshe kuma budurwa Adeyemi ce.

Saurayin diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo ya samu masauki a kurkuku

Saurayin diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo ya samu masauki a kurkuku

DUBA WANNAN: Yadda wani dan shekaru 17 ya tsira daga gidan matsafa a Kano

Adeyemi tare da wasu mutane biyu ne suka hada baki suka yiwa Khadijat kisar gilla a dakin Adeyemi kuma suka birne gawarta a karkashin gadonsa a gidansa dake unguwar Aratusin dake Akure kafin daga baya aka kama shi.

An gurfanar da Adeyemi ne a gaban kotu a ranar Litinin 16 ga watan Yuli inda ake tuhumarsa da aikata laifuka biyu na hadin baki da kisar gilla.

A yayin gudanar da shari'ar, Dan sanda mai shigar da kara, Saja Mary Adebayo ta bukaci kotu ta tsare wanda ake tuhumar a kurkuku gabanin lokacin da za'a samu shawarar lauyoyi daga sashin hulda da jama'a DPP.

Lauya mai kare wanda ake tuhuma, Taiwo Gbadebo, baiyi jayaya da bukatar da lauya mai shigar da kara ya nema ba.

Hakan yasa Alkalin kotun, Mrs Victoria Bob-Manuel, ta bayar da umurnin a tsare Adeyemi a gidan yari har sai an samu shawarar lauyoyi daga sashin hulda da jama'a, DPP.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel