Karyar walwalar ciki ta kare tunda 'Fayose' ya fadi zabe - Farfesa Sagay

Karyar walwalar ciki ta kare tunda 'Fayose' ya fadi zabe - Farfesa Sagay

Shugaban kwamitin dake bawa shugaban kasa shawara kan hana rashawa (PACAC) ya yabawa al'ummar jihar Ekiti kan yadda suka hambarar da gwamnatin PDP a zaben da akayi ranar Asabar da ta gabata inda ya kara da cewa faduwar dan takarar Fayose zai kawo karshen karyar yaudarar walwalar ciki a jihar.

Sagay ya yi wannan furuci ne yayin wata hira da ya yi da Saharar reporters a jiya Litinin.

Ciyaman din na PACAC ya bayyana gwamna Ayodele Fayose a matsayin mutum da ya yi amfani da talauci da fatara da mutanen jihar ke ciki wajen biyan bukatun kansa.

Karyar walwalar ciki ta kare tunda 'Fayose' ya fadi zabe - Farfesa Sagay

Karyar walwalar ciki ta kare tunda 'Fayose' ya fadi zabe - Farfesa Sagay

DUBA WANNAN: Soji sun kamo masu sayar wa da Boko Haram 'kayan aiki'

Ya ce, "Ina kyautata zaton mutanen Ekiti sun kwato wa kansu mutunci da darajarsu bayan zaben Ayo Fayose wanda ya ci zarafinsu da cewa ya yi nasarar cin zabe ne saboda ya yi musu alkawarin rabon kudi da abinci.

"Babban cin mutunci ne cewar da ya yi mutanen Ekiti suna rayuwa ne kawai saboda su ci abinci. Hakan yasa siyasar walwalar ciki cin fuska ce. Ya yi musu irin wannan cin fuskar na tsawon shekaru hudu; duk ya karya tattalin arzikin jihar.

"Baya biyan albashi, gaba daya dai mulkinsa duk abin takaici ne. Kayar da mataimakinsa a zaben daidai yake da kayar da Fayose saboda bana tsamanin mataimakinsa ne aininhin dan takarar."

Sagay ya shawarci Fayose da tawagarsa suyi watsi da batun zuwa kotu su rungumi kadara.

Ya ce lokacin da jam'iyyar PDP su kayi magudin zabe a shekarar 2014, Fayose baiyi korafi ba "amma yanzu yana ta kururuwa saboda shine ya fadi zaben."

Babban lauyan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda yan siyasa suka rika sayan kuri'u da kudi amma yace hakan ba zai canja sakamakon zaben ba tunda dukkan bangarorin sun raba kudaden.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel