Yanzu-yanzu: Dasuki ya cika sharrudan beli, za’a sakeshi yau - Lauya

Yanzu-yanzu: Dasuki ya cika sharrudan beli, za’a sakeshi yau - Lauya

Tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Kanal Sambo Dasuki, ya cika dukkan hsarrudan belin da babban kotun tarayya da ke Abuja ta bashi ranan 2 ga watan Yuli, 2018, game da cewar lauyansa, Mr. Ahmed Raji (SAN).

Mr. Ahmed Raji ya ce mataimakin magatakardan babban kotun tarayya ya tabbatar da cewa Dasuki ya cika sharrudanbelin kuma a yau (Talata), a’a mikawa hukumar DSS da suka tsareshi tun Disamban 2015.

Lauyan yayinda yake amsa tambaya daga jaridar Punch ya bayyana cewa ana sa ran za’a sakeshi muddin sun mika wasikar kotu ga DSS da safen nan.

Raji yace: “Wasikar da mataimakin magatakardan kotun na tabbatar da cewa an cika dukkan sharrudan beli zai shiga hannun hukumar DSS da safen nan.”

“Idan muka kai musu, DSS za ta sakeshi bisa ga umurnin kotu.”

A ranan 2 ga wtaan Yuli, babban kotun tarayya dake zaune a Abuja, ta baiwa Kanal Sambo Dasuki beli bayan an garkameshi na tsawon shekaru 2.

Jastis Ijeoma Ojukwu, wacce ta bada belin ta bada sharrudan biyan N200m da masu tsaya masa guda 2.

Duk da cewa Dasuki ya bukaci gwamnati ta bashi hakuri tare da diyyar N5bn, Jastis Ijeoma Ojukwu, ta yi watsi da wannan bukata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel