APC ta aika sammaci ga Akume da Ortom zuwa Abuja

APC ta aika sammaci ga Akume da Ortom zuwa Abuja

Mataimakin jam’iyyar APC na kasa(Arewa), Sanata Lawal Shu’aibu ya aika sammaci ga Gwamna Samuel Ortom da Sanata George Akume, manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a jihar Benue domin wata ganawa a Abuja.

An kira taron ne bayan wata sanarwa daga gwamnan dake cewa ya fice daga jam’iyyar.

Daga Ortom hr Akume, tsohon gwmnan jihar, su kasance a takun saka saboda jan ragamar kula da jam’iyyar.

APC ta aika sammaci ga Akume da Ortom zuwa Abuja

APC ta aika sammaci ga Akume da Ortom zuwa Abuja

A ranar Litinin, 16 ga watan Yuli ne Gwamna Ortom jim kadan bayan rantsar d Mista Jerome Shimbe ya sanar da ficewarsa daga APC.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin Najeriya tayi asarar manyan kwamandojin ta 10 a jihar Borno

A cewar gwmnan, ya fice daga APC ne bayan an basa jan katin barin jam’iyyar.

Ya ce wannan kati zi bashi damar komawa ko wacce jam’iyyaar da yake ganin ta cancanta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel