Kungiyar Hakika: Hukumar yan sanda ta kaddamar da bincike

Kungiyar Hakika: Hukumar yan sanda ta kaddamar da bincike

Hukumar yan sandan Najeriya, shiyar jihar Nasarawa ta bayyana cewa an kaddamar da binciken leken asiri kan tsirowar wata sabuwar kungiyar addini mai suna ‘Hakika’ a karama hukumar Toto na jihar.

Jaridar New Telegraph ta bada rahoton cewa mutanen karamar hukumar sun kasance cikin firgici bayan tsirowar kungiyar da kuma yadda ya bayyana a kafafun yada labarai.

A wani hira da da manema labarai, kakakin hukumar yan sandan jihar Nasarawa, Sama’aila Usman, yace jami’an leken asiri sun bazama cikin garin domin gano ainihin yadda kungiyar ta tsiro da kuma yadda abubuwan suke.

Kungiyar Hakika: Hukumar yan sanda ta kaddamar da bincike

Kungiyar Hakika: Hukumar yan sanda ta kaddamar da bincike
Source: Depositphotos

Ya ce duk da cewa hukumar bata samu wani kara kan yan kungiyar ba, ta dauki wannan matakin ne domin gano gaskiyan al’amarin.

KU KARANTA: Jerin gwamnonin Arewa 5 da ka iya faduwa zaben 2019

Kakakin hukumar ya yi kira da jama’a sun kwantar da hankulansu kuma su cigaba da rayuwarsu nay au da kullum.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa hukumar sojin Najeriya ta saki jawabi kan tsirowar wasu yan kungiyar Hakika a Arewacin Najeriya.

Jawabin hukumar soji ya kara da cewa wadannan yan Hakikan duk da cewa suna ikirarin cewa mabiya addinin Musulunci ne, ba sa Sallah.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel