Fayose zai gurfana a kotu bayan karewan wa’adinsa - EFCC

Fayose zai gurfana a kotu bayan karewan wa’adinsa - EFCC

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta bayyana a jiya Litinin cewa gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, zai gurfana gaban hukuma bayan karewa wa’adinsa a watan Oktoba.

Mr Fayose. Wanda ya kasance babban dan adawan shugaba Muhammadu Buhari zai kare wa’adinsa ne a watan Oktoba inda zai mika ragamar mulki ga gwamna mai jiran gado kuma tsohon ministan ma’adinai, Kayode Fayemi.

A ranan Asabar da ya gabata, Fayemi ya lallasa dan takaran jam’iyyar PDP kuma mataimakin gwamnan jihar Ekiti, Kolapo Olusola.

KU KARANTA: Jerin gwamnonin Arewa 5 da ka iya faduwa zaben 2019

Amma gwamna Fayose, mataimakinsa, da jam’iyyar PDP, sun lashi takobin cewa zasu kalubalanci wannan sakamako a kotun zabe.

Fayose zai gurfana a kotu bayan karewan wa’adinsa - EFCC

Fayose zai gurfana a kotu bayan karewan wa’adinsa - EFCC

A wani jawabi da EFCC ta turawa kafafan yada labarai a daren jiya, kakakin hukumar EFCC , Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa lallai Fayose zai fukanci gurfana bayan karewa wa’adinsa.

Yace: “Duk da cewan akwai tuhume-tuhume akan gwamna Fayose, babban kotun tarayya da ke zaune a jihar Ekiti zata gurfanar da shi bayan karewan wa’adina, ba EFCC ba,”.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa hukumar EFCC ta saki maganan barazana ga gwamnan jihar Ekiti bayan hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben kuma ya bayyana cewa an kayar da Fayose.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel