Kashe-Kashe: Wani babban malamin addini ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari

Kashe-Kashe: Wani babban malamin addini ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari

Shugaban majami'un darikar Roman Katolika na garin Abuja, babban binin tarayya mai suna John Cardinal Olaiyekan ya bayyana cewa bishop-bishop din Najeriya tuni suka yanke kauna da samun shugabanci na gari daga shugaba Buhari.

John Cardinal ya bayyana hakan ne a garin Ilorin na jihar Kwara lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala nadin shugaban majami'un Roman Katolikan jihar Bishop Paul Olawoore.

Kashe-Kashe: Wani babban malamin addini ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari

Kashe-Kashe: Wani babban malamin addini ya yi kaca-kaca da Shugaba Buhari

KU KARANTA: An hana kafa allon kamfe na Dankwambo a wannan jihar ta Arewa

Legit.ng ta samu cewa ya kara da cewa kafin zuwan wannan gwamnatin sun yi tsammanin za su samu shugabanci na gari amma sai lamarin ya zo masu ba haka ba.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a jihar shugaban kasa ta Katsina a can yankin Arewa maso yammacin Najeriya sun sanar da samun nasarar damke wani gawurtaccen marawon motoci da motocin sata har biyu.

Wanda aka kama da motocin da ake kyautata zaton na sata ne, mai suna Wadatau Lawan dan asalin jihar Sokoto ne kamar dai yadda jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, SP Gambo Isa ya sanar da manema labarai a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel