Zaben 2019: An hana kafa allon kamfe na Dankwambo a wata jihar Arewa

Zaben 2019: An hana kafa allon kamfe na Dankwambo a wata jihar Arewa

Kamar dai yadda muka samu a labarai, gwamnatin jihar Adamawa dake a shiyyar Arewa ta gabas a Najeriya ta bayar da umurnin haka kafa allunan kamfe dauke da hotunan gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo a dukkan fadin jihar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takarda da hukumar kula da taswirar gine-ginen jihar watau State Urban Planning ta fitar tare da aikewa da ita a ofishin kamfe din Dankwambon a jihar.

Zaben 2019: An hana kafa allon kamfe na Dankwambo a wata jihar Arewa

Zaben 2019: An hana kafa allon kamfe na Dankwambo a wata jihar Arewa

KU KARANTA: Obasanjo ya fadi dalilin da ya sa ya bar PDP a baya

Legit.ng ta samu cewa sai dai tuni lamarin ya jawo muhawa mai zafi a tsakanin magoya bayan dan takarar da kuma mahukuntan jihar inda suka nuna rashin jin dadin su game da hakan.

A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a jihar shugaban kasa ta Katsina a can yankin Arewa maso yammacin Najeriya sun sanar da samun nasarar damke wani gawurtaccen marawon motoci da motocin sata har biyu.

Wanda aka kama da motocin da ake kyautata zaton na sata ne, mai suna Wadatau Lawan dan asalin jihar Sokoto ne kamar dai yadda jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, SP Gambo Isa ya sanar da manema labarai a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel