Tabbas za mu yi kewar ka a tare da mu - Gwamnonin Najeriya zuwa ga Fayose

Tabbas za mu yi kewar ka a tare da mu - Gwamnonin Najeriya zuwa ga Fayose

Kungiyar Gwamnonin jihohin Najeriya a ranar Litinin din da ta gabata sun bayyana cewa tabbas za suyi kewar gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Mista Ayodele Fayose tare kuma da yin maraba da sabon gwamnan jihar mai jiran gado, Kayode Fayemi.

Mataimakin shugaban gwamnonin, kuma gwamnan jihar Zamfara na musamman a kar harkokin yada labarai shine ya sanar da hakan a wata sanarwar manema labarai da ya fitar a madadin gwamnan.

Tabbas za mu yi kewar ka a tare da mu - Gwamnonin Najeriya zuwa ga Fayose

Tabbas za mu yi kewar ka a tare da mu - Gwamnonin Najeriya zuwa ga Fayose

KU KARANTA: Shugabannin kasashe 10 mafi arziki a duniya

Legit.ng ta samu cewa a cikin takardar manema labaran dai, gwamnan ya yabawa gwamnan mai barin gado akan irin yadda ya sadaukar da rayuwar sa wajen kyautata rayuwar 'yan jihar ta sa.

A wani labarin kuma, Wasu mafusatan matasa da ake kyautata 'yan zauna gari banza ne sun jefi kwamishinan 'yan sanda a jihar Taraba dake a yankin Arewa maso gabashin kasar nan mai suna David Akinremi har suka fasa masa kai.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan a jihar David Misal shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a garin Jalingo, babban birnin jihar inda ya ce lamarin ya auku ne lokacin da kwamishinan ya kai wata ziyarar aiki zuwa ungiwar Tudun wada.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel