'Yan sanda a wata jihar arewa sun kama gawurtaccen barawon motoci da motocin sata 2

'Yan sanda a wata jihar arewa sun kama gawurtaccen barawon motoci da motocin sata 2

Jami'an 'yan sandan Najeriya dake a jihar shugaban kasa ta Katsina a can yankin Arewa maso yammacin Najeriya sun sanar da samun nasarar damke wani gawurtaccen marawon motoci da motocin sata har biyu.

Wanda aka kama da motocin da ake kyautata zaton na sata ne, mai suna Wadatau Lawan dan asalin jihar Sokoto ne kamar dai yadda jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, SP Gambo Isa ya sanar da manema labarai a jihar.

'Yan sanda a wata jihar arewa sun kama gawurtaccen barawon motoci da motocin sata 2

'Yan sanda a wata jihar arewa sun kama gawurtaccen barawon motoci da motocin sata 2

KU KARANTA: Kwamitin mutum 11 zai binciki Obasanjo da Jonathan

Legit.ng ta samu cewa da yake karin bayani, SP Gambo ya bayyana cewa jam'ian nasu na 'yan sanda sun cafke barawon ne a garin Malumfashi na jihar kuma yanzu haka suna kan binciken lamarin.

A wani labarin kuma, Majiyar mu da muka tabbatar, ta labarta mana cewa kawo yanzu dai jami'an rundunar sojin Najeriya dake fafatawa da 'yan Boko Haram a garin Bama na jihar Borno sun gano gawawwakin 'yan uwan su kusan 10 biyo bayan samamen da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai masu.

Wannan dai na zuwa ne duk kuwa da yadda jami'an rundunar suka fito suka karyata labarin kai harin da ya bulla a kafafen yada labaran kasar a jiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel