Rundunar sojin Najeriya tayi asarar manyan kwamandojin ta 10 a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya tayi asarar manyan kwamandojin ta 10 a jihar Borno

Majiyar mu da muka tabbatar, ta labarta mana cewa kawo yanzu dai jami'an rundunar sojin Najeriya dake fafatawa da 'yan Boko Haram a garin Bama na jihar Borno sun gano gawawwakin 'yan uwan su kusan 10 biyo bayan samamen da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai masu.

Wannan dai na zuwa ne duk kuwa da yadda jami'an rundunar suka fito suka karyata labarin kai harin da ya bulla a kafafen yada labaran kasar a jiya.

Rundunar sojin Najeriya tayi asarar manyan kwamandojin ta 10 a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya tayi asarar manyan kwamandojin ta 10 a jihar Borno

KU KARANTA: "Allah ya ce APC da PDP su ni tikitin takarar shugaban kasa a 2019"

Legit.ng ta samu daga jaridar Punch cewa kawo yanzu dai an ga gawawwakin jami'an 10 sannan kuma ana cigaba da neman sauran.

A wani labarin kuma, Kamar dai yadda muka samu a labarai, gwamnatin jihar Adamawa dake a shiyyar Arewa ta gabas a Najeriya ta bayar da umurnin haka kafa allunan kamfe dauke da hotunan gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo a dukkan fadin jihar.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata takarda da hukumar kula da taswirar gine-ginen jihar watau State Urban Planning ta fitar tare da aikewa da ita a ofishin kamfe din Dankwambon a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel