Babu ruwan ‘Yan kasar waje a wajen kashe-kashen Najeriya - Jakadan Faransa

Babu ruwan ‘Yan kasar waje a wajen kashe-kashen Najeriya - Jakadan Faransa

- Denys Gauer yace babu ruwan ‘yan waje a kashe-kashen da ake yi a Najeriya

- Gauer wanda shi ne Jakadan Faransa a nan Najeriya yace rikicin na gida ne

- Jakadan ya nemi Gwamnati ta hukunta duk wanda aka samu da laifin kisa

Jakadan kasar Faransa da ke Najeriya Denys Gauer yayi bayani game da kashe-kashen da ake yi a Najeriya inda ya bayyana cewa sam bai yarda wasu baki ne ke shigowa su na wannan ta’adi ba.

Babu ruwan ‘Yan kasar waje a wajen kashe-kashen Najeriya - Jakadan Faransa

Jakadan Faransa mai shirin barin Najeriya Gauer

Denys Gauer wanda shi yake wakiltar Kasar Faransa a Najeriya yayi wannan jawabi ne a wajen wani taro na musamman na Mutanen Kasar ta Faransa da aka yi a babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja a cikin makon jiya.

Jakadan wanda yanzu ya fara shirin tattara kayan sa ya bar Najeriya ya koma gida, yace rikicin kasa ya jawo wannan kashe-kashe ba komai ba. Dalilin haka ne Jakadan ya nemi Gwamnati ta inganta harkar noma da kiwo.

KU KARANTA:

Bayan nan kuma Jakadan na Kasar Turan ya bayyana cewa rashin hukunta wadanda aka samu da laifi yana cikin abin da yake hura wutan rikicin da ake yi a Kasar. Wannan jawabi na Jakadan ya sabawa matsayin Gwamnatin kasar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saba nuna cewa wasu bakin tsagera ne musamman daga irin su Kasar Libiya su ka hauro Najeriya su ke barna. Denys Gauer yace bai yarda da wannan magana ba don kuwa ta’adin ‘Yan gida ne.

Jakadan Faransa ya ba Gwamnatin Najeriya shawara kan rikicin Makiyaya, Jakadan ya karyata Shugaba Buhari na cewa tsagera ne musamman daga irin su Kasar Libiya su ka hauro Najeriya su ke barna a cikin Kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel