Idan har baka gamsu da sakamakon zaben ba kaje kotu – INEC ga dan takarar gwamnan Ekiti

Idan har baka gamsu da sakamakon zaben ba kaje kotu – INEC ga dan takarar gwamnan Ekiti

- Alamu na nuna cewa tsugunno bai kare ba dangane da zaben Ekiti

- Jam'iyyar PDP da dan takararta sunyi watsi da sakamakon zaben bayan sun sha kaye

- Bisa kalaman nasu ne kuma INEC ta kalubalancesu da su je kotu

Hukumar zabe ta kasa INEC ta mayarwa da dan takarar PDP na jihar Ekiti martani da cewa yana da damar da zai kai korafinsa zuwa ga kotun koli domin neman hakkinsa in har bai yarda da sakamakon zaben da aka gudanar ba wanda dan takarar jam'iyyar APC ya lashe.

Idan har baka gamsu da sakamakon zaben ba kaje kotu – INEC ga dan takarar gwamnan Ekiti

Idan har baka gamsu da sakamakon zaben ba kaje kotu – INEC ga dan takarar gwamnan Ekiti

Hakan yana fito daga bakin wakilin hukumar zaben da ya jagoranci yadda aka gudanar da zaben, Farfesa Kolapo Olusola –Eleka, inda yace sakamakon zaben ba komai bane face abinda mutane suke so kuma shi suka zaba.

A jiya ne dai gwamnan jihar Adoyele Fayose ya kalubalanci sakamakon, inda ya bayyana murnar da dan takarar APC ke yi a matsayin ta dan wani lokaci domin nan bada jimawa ba zasu mika kokensu zuwa ga kotun koli.

KU KARANTA: Dalilin da yasa zan goyi bayan Buhari a zaben 2019 Satguru Maharaj Ji

Shi ma shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya tofa albarkacin bakinsa inda ya ce "Wannan abu ne mai matukar amfani saboda a karkashin shugaba Buhari mun gani za a iya yin zabe ba tare da fargabar cutar da mutane ba balle har su rasa rayukansu duk a dalilin zaben wanda suke son ya shugabance su a yayin kada kuri'a".

Idan har baka gamsu da sakamakon zaben ba kaje kotu – INEC ga dan takarar gwamnan Ekiti

Idan har baka gamsu da sakamakon zaben ba kaje kotu – INEC ga dan takarar gwamnan Ekiti

Oshiomhole ya kara da cewa "Ba wai muna murna saboda jam'iyyarmu tayi nasara bane, face abu ne ya fito fili saboda jama'a sun zabi wanda suke so wannan kuwa babbar nasara ce ga jama'ar jihar Ekiti".

"A wannan zaben idan aka duba za a ga yadda dimukuradiyya ta taka rawar gani, ba wai sai wanda kake so ya yi nasara ba, bukatar shi ne zaben wanda zai yi abinda ake bukata kuma muna da yakinin Fayemi zai cika wannan aiki da muke sa rai".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel