Sabon salo: INEC ta kawo yadda za ayi maganin satar kayan zabe

Sabon salo: INEC ta kawo yadda za ayi maganin satar kayan zabe

Labari ya zo mana kwanan nan cewa a wani yunkuri wanda shi ne na farko a tarihi, Hukumar zabe na kasa watau INEC ta kawo wani tsarin da zai yi maganan satar kayan zabe a kasar nan.

Hukumar INEC wanda nauyin gudanar da zabe ya rataya a kan ta a Najeriya ta kirkiro wata sabuwar fasahar zamani da za ta sa a kawo karshen magudi a Kasar nan. Wannan fasaha zai ki maganin satar kayan aikin zabe.

Sabon salo: INEC ta kawo yadda za ayi maganin satar kayan zabe

Hukumar zabe na kasa ta INEC ta kawo wani gyara

INEC ta kirkiro fasahar da za ta sa a rika ganin duk inda aka tafi da kayan aikin zabe tun daga lokacin da su ka bar ofishin zaben har zuwa inda za ayi amfani da su. Wata na’ura ce za ta rika bayyana duk inda aka shiga da kayan zaben.

KU KARANTA: Wani Malamin addini ya fito takara a Najeriya

A lokacin zaben sabon Gwamnan Jihar Ekiti da aka yi cikin ‘yan kwanakin nan ne aka kaddamar da wannan tsari domin maganin masu magudi musamman a Jam’iyyar APC mai mulki da kuma babbar Jam’iyyar adawa watau PDP.

Yanzu dai duk inda aka tafi da kayan aikin zaben, Jami’an Hukumar INEC za su samu labari a nau’rar aikin su. Sanannen abu ne cewa wasu kan yi amfani wajen sungume kayan zabe su tsere da shi domin a murde sakamakon zabe a kasar.

Yanzu dai an fara shirin yadda za a tsaida sabon Gwamna a Jihar Osun, tuni dai har Hukumar zabe na kasar watau INEC ta sa ranar zabe inda ake sa rai za a fitar da sabon Gwamna a watan jibi na Satumba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel