Jam’iyyar APC ta fara shirin lashe zaben Gwamnan Jihar Osun

Jam’iyyar APC ta fara shirin lashe zaben Gwamnan Jihar Osun

Yanzu dai an fara shirin yadda za a fitar da gwani na Takarar Gwamna a Jihar Osun a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki. Tuni ma dai har INEC ta sa ranar zabe inda za a fitar da sabon Gwamna a karshen watan Satumban nan mai zuwa.

Jam’iyyar APC ta fara shirin lashe zaben Gwamnan Jihar Osun

Jam'iyyar APC ta fara neman Magajin Gwamna Aregbesola

Jam’iyyar APC mai mulki za ta yi zaben fitar da gwanin ta ne a Ranar Alhamis inda za ta tsaida ‘Dan takarar da za ta ba tuta. Sai dai kwanaki mai magana da yawun bakin Jam’iyyar watau Bolaji Abdullahi yace har yanzu su na da sauran aiki.

Sakataren yada labaran APC na kasa Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa Jam’iyyar ba ta cin ma matsayar yadda za ta gudanar da zaben ba. Ana dai sa ran a makon nan ne Shugabannin Jam’iyyar za su zauna domin su fara shiryawa zaben na Osun.

KU KARANTA: Za mu hana magudin zabe - Jam'iyyar PDP

Wasu na neman ganin an yi yadda aka saba a da wajen tsaida ‘Dan takarab. Masu goyon bayan wannan tsari su na tare ne da Sakataren Gwamnatin Jihar Osun Alhaji Moshood Adeoti inda wasu kuma su ka nemi kowane ‘Dan APC ya fito yayi zabe.

Gwamnan Osun mai shirin ajiye mulki Rauf Aregbesola da kuma Shugaban Ma’aikatan gidan Gwamnatin Jihar watau Alhaji Gboyega Oyetola, su na nema ne su ga an bada dama kowane ‘Dan Jam’iyya ya zabi wanda za a ba tikitin tsayawa Gwamna.

Jiya kun ji cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta fara neman ganin yadda za ta samu nasara a Jihohi Gombe da Taraba a zaben 2019. Jihohin dai yanzu su na hannun PDP ne. Hakan na zuwa ne bayan Jam’iyyar mai mulki ta lashe zaben Ekiti da aka yi a makon jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel