Majalisa: Ku sake yi wa kasafin kudin 2018 wani kallo – Buhari

Majalisa: Ku sake yi wa kasafin kudin 2018 wani kallo – Buhari

- Shugaban kasa Buhari yayi magana a kan kasafin kudi na 2018

- Shugaban Kasar ya nemi Majalisar ta sake kallon kasafin na bana

- Sakataren Gwamnatin Najeriya ne ya gayyaci Buhari wajen taro

Mun samu labari dazu cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Tarayya ta sake duban kundin kasafin wannan shekarar na 2018. Shugaban Kasar ya bayyana wannan ne a babban Birnin Tarayya Abuja.

Majalisa: Ku sake yi wa kasafin kudin 2018 wani kallo – Buhari

Shugaba Buhari ya ji takaicin matsalolin da aka samu bana

Kamar yadda Jaridar nan ta Daily Trust ta kasar nan ta rahoto, Shugaban Kasar ya nemi Sanatoci da ‘Yan Majalisun Tarayya cewa su bibiyi wuraren da yace akwai matsala lokacin da zai sa hannu kan kundin kasafin na bana.

KU KARANTA: Ba a fahimci aikin Majalisa a Najeriya ba - Dogara

Sakataren Gwamnatin Tarayya Mista Boss Mustapha ne ya wakilci Shugaban Kasar a wani zama da aka ayi da ‘Yan Majalisun Kasar. Boss yace bai ji dadin yadda ‘Yan Majalisun su ka gaza yin aikin da ya dace game da kasafin kasar ba.

Boss Mustapha ya koka da yadda aka gaza shawo kan matsalolin da ake samu tsakanin fadar Shugaban kasar da kuma ‘Yan Majalisun Tarayya. Majalisar ta koka da wannan batu ita ma, kuma Shugaban kasar yace za a duba lamarin a gyara.

Muhammadu Buhari yayi wannan bayani ne wajen wani mako da Majalisar ta shirya inda a baya ta zarge ta da cusa wasu ayyuka a kasafin bana. Shugabannin Majalisar dai sun nemi a hada kai ayi tare domin ganin cigaban kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel