2019: Za mu yi duk wacce za mu yi domin ganin ba’a yi magudin zabe ba - PDP

2019: Za mu yi duk wacce za mu yi domin ganin ba’a yi magudin zabe ba - PDP

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta gargadi fadar shugaban kasa da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan cewa kada ta yi kuskuren tunanin ko yan Najeriya sun amince da magudin zaben Ekiti.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta saki a ranar Litinin ta hannun kakkakinta, , Kola Ologbondiyan, ta bayyana cewa za ta yi duk abunda ya kamata domin ganin ba’a yi magudin zabe ba tunda a yanzu ta san halin APC.

2019: Za mu yi duk wacce za mu yi domin ganin ba’a yi magudin zabe ba - PDP

2019: Za mu yi duk wacce za mu yi domin ganin ba’a yi magudin zabe ba - PDP
Source: Depositphotos

A cewar su hakan ba zai taba yiwuwa ba domin yan Najeriya sun rigada sun yanke shawarar canza sabon shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka: Bamu kori Ortom daga jamiyyarmu a – APC ta maida martani

Jam’iyyar ta jaddada cewa Najeriya ta fi karfin wani kungiya ko wasu mutane su yi mata magu-magu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel