Yan Najeriya sun jahilci matsayin majalisar dokoki - Dogara

Yan Najeriya sun jahilci matsayin majalisar dokoki - Dogara

Kakakin majalisar wakilai, Mista Yakubu Dogara, ya bayyana cewa yan Najeriya da dama basu san ayyukan majalisa ba wajen aiwatar da manufofin da kundin tsarin mulki ya gindaya.

Dogara ya bayyana hakan a ranar Litinin a wajen bude taron majalisar dokokin kasa A Abuja.

Ya bayyana cewa taron zai ba da damar da za’a sanar da yan Najeriya Karin ayyukan majalisun da sauran ayyuka.

Yan Najeriya sun jahilci matsayin majalisar dokoki - Dogara

Yan Najeriya sun jahilci matsayin majalisar dokoki - Dogara

Dogara ya kuma bayyana cewa bangaren dokoki ne mafi muhimmanci a rukunin gwamnati saboda duk wani damokradiya ya fara sannan yak are da dokoki.

KU KARANTA KUMA: Sauya sheka: Bamu kori Ortom daga jamiyyarmu a – APC ta maida martani

Ya kara da cewa za’a cimma gwamnati mai inganci da ci gaba ne kawai idan har bangarori uku na gwamnati suka yi aiki yadda ya kamata sannan suka girmamma ka’ida da doka.

Kakakin majalisan yace ya kamata bangarorin gwamnati su mutuntu juna tare da kwana da sanin cewa ra’ayi baida alaka da jagorantar damokradiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel