Jama’a da dama sun mutu yayin da aka kaiwa kwamishinan ‘yan sanda hari a Jalingo

Jama’a da dama sun mutu yayin da aka kaiwa kwamishinan ‘yan sanda hari a Jalingo

Da safiyar yau ne wasu kangararrun matasa suka kaiwa David Akinremi, kwamishinan ‘yan sandan jihar Taraba hari tare da jifansa a ka.

Lamarin ya faru ne a wani yankin unguwar Tudun Wada dake Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

An garzaya da kwamishinan ‘yan sandan asibiti kafin daga bisani a sallame shi.

Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar Taraba, David Mishal, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da sanar da cewar kwamishina Akinremi na cikin koshin lafiya.

Jama’a da dama sun mutu yayin da aka kaiwa kwamishinan ‘yan sanda hari a Jalingo

Jama’a da dama sun mutu yayin da aka kaiwa kwamishinan ‘yan sanda hari a Jalingo

Misal ya bayyana cewar kwamishinan ya je yankin ne domin tabbatar da doka da oda bayan barkewar wani rikici tsakanin wasu matasa.

An kama jama’a da dama yayin da rahotanni suka bayyana cewar ‘yan sanda sun kasha matasa da dama. Saidai Kakakin ‘yan sandan y ace bashi da masaniyar hakan.

DUBA WANNAN: Bayan kammala zaben Ekiti, Obasanjo ya sake rangada wata doguwar wasikar

Misal ya yi gargadin cewar hukumar ‘yan sanda ba zata zuba ido yayin da wasu ‘yan tsirarun batagari ke daukan doka a hannunsu ba.

Zan yi amfani da wannan dama nayi kira ga jama’a das u sanar da jami’anmu duk wani yunkurin tayar da hankali domin daukan mataki a kan lokaci,” acewar Mishal.

Ko a ranar Lahadi saida wasu kangararrun matasa suka kaiwa tawagar gwamnan jihar Filata, Simon Lalong, farmaki a hanyarsa ta kai ziyara wani sansanin ‘yan gudun hijira.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel