Badakalar N2.9bn: Babbar kotu ta umarci alkali ya yankewa wani tsohon gwamna hukunci kafin watan Satumba

Badakalar N2.9bn: Babbar kotu ta umarci alkali ya yankewa wani tsohon gwamna hukunci kafin watan Satumba

- Shugaban kotun daukaka kara ta bayar da umarnin a yankewa tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Kalu, hukunci kafin watan Satumba

- Ana tuhumar da Kalu da badakalar karkatar da kudin Abiya biliyan N2.9 lokacin day a mulki jihar daga shekarar 1999 zuwa 2007

- Kalu ya musanta dukkan tuhuma 34 da ake yi masa a gaban kotun

Shugabar kotun daukaka kara, Zainab Bulkachuwa, ta bayar da umarnin a yankewa tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Kalu, hukunci kafin karshen watan Satumba na shekarar nan, 2018.

Jastis Mohammed Idris, alkalin kotun da aka gurfanar da Orji Kalu, ya sanar da hakan yayin da kotun ta zauna yau domin cigaba da sauraron karar a Legas.

Badakalar N2.9bn: Babbar kotu ta umarci alkali ya yankewa wani tsohon gwamna hukunci kafin watan Satumba

Orji Uzor Kalu

Farfesa Awa Kalu, lauyan dake kare Kalu ne ya rubuta takardar neman Bulkachuwa ta bawa Jastis Idris dammar cigaba da sauraron karar da aka dade ana fafatawa.

DUBA WANNAN: Jan aiki: Fadar shugaban kasa ta dorawa Kachikwu alhakin warware rigingimun APC

Lauyan ya mika wannan bukata ne ga Bulkachuwa bisa dogaro da sashe na 396(7) da ya bawa alkalin da aka yiwa karin girma damar karasa dukkan shari’ar dake hannunsa kafin a yi masa karin girman.

Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ce ta gurfanar da Kalu tare da wani kamfaninsa bisa zargin karkatar da kudin jihar Abiya, biliyan N2.9bn, lokacin da yake gwamna daga 1999 zuwa 2007.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel