Fashi da makami: Sanata Wamakko ya bayar da tallafin kayayyakin agaji na N2m ga wadanda abun ya shafa a Sokoto

Fashi da makami: Sanata Wamakko ya bayar da tallafin kayayyakin agaji na N2m ga wadanda abun ya shafa a Sokoto

Shugaban kungiyar sanatocin Arewa, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayar da tallafin kayayyakin abinci da sauran abubuwa wanda farashin su ya kai naira miliyan biyu ga wadanda kashe-kashen Tabanni, karamar hukumar Rabah na jihar Sokoto ya cika da su.

Ya bayyana lamarin a matsayin abun da zai taba zuciyar duk wani mutum mai tunani.

Da yake Magana a lokacin da ya ziyarci sansanin yan gudun hijira a Gandi, ya yi korafin cewa wannan asarar rayuka da dukiyoyi da akayi abun kaico ne.

Fashi da makami: Sanata Wamakko ya bayar da tallafin kayayyakin agaji na N2m ga wadanda abun ya shafa a Sokoto

Fashi da makami: Sanata Wamakko ya bayar da tallafin kayayyakin agaji na N2m ga wadanda abun ya shafa a Sokoto

Ya bukaci jama’a das u dage da addu’a domin guje ma sake faruwar lamarin, inda ya kara da cewa za’ayi kokarin ganin an ba yan Najeriya da dukiyoyinsu kariya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sanatan Adamawa da wani dan majalisa 1 sun bar APC, sun koma ADC

Dan majalisan ya kuma yabama gwamnatin jihar Sokoto, da hukumar bayar da tallafin Zakkah na jihar, bisa kokarinsu na samar da kayan jin dadi da tsaron da mutanen ke bukata a sansanin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel