An tura jami'an tsaro yankin da 'yan fashi suka yi barazanar kai hari a jihar Lagos

An tura jami'an tsaro yankin da 'yan fashi suka yi barazanar kai hari a jihar Lagos

Biyo bayan barazanar da wadansu 'yan fashi da makami suka yiwa mutanen wasu yankuna dake jihar Legas, kwamishinan yan sandan jihar ta Legas, Imohimi Edgal, ya tura jami'an 'yan sanda yankin domin tabbatar da tsaro

An tura jami'an tsaro yankin da 'yan fashi suka yi barazanar kai hari a jihar Lagos

An tura jami'an tsaro yankin da 'yan fashi suka yi barazanar kai hari a jihar Lagos
Source: Depositphotos

Biyo bayan barazanar da wadansu 'yan fashi da makami suka yiwa mutanen wasu yankuna dake jihar Legas, kwamishinan yan sandan jihar ta Legas, Imohimi Edgal, ya tura jami'an 'yan sanda yankin domin tabbatar da tsaro a wurin.

Ofishin jakadancin labarai ya ruwaito cewa mazauna yankin Igando, Egan, Akesan da Obadore an kai musu harin fashi da makami, inda kuma yan fashin suka aika da wasika cewa su tsammanci wani zuwan nasu.

DUBA WANNAN: Ta hana a yiwa diyarta magani saboda tana so take amfani da ita tana karbar sadaka

A wata ziyara da kwamishinan ya kai wa mutanen da abin ya shafa a ranar Litinin dinnan, yace sabon DPO zai fara aiki kuma jami'an yan sandan da suka yi shekaru 3 suna aiki a yankin za a dauke su.

"Na kira taron gaggawa ne saboda yanayin tsarin aikina, wanda shine amfani da yan sandan yanki. Nasan muna da matsalar tsaro kuma zamu iya magance ta tare.

"An sanar dani cewa bata gari suna damun mutanen yankin nan. Nazo ne don daidaita abubuwa.

"Nasan DPO din yankin nan yana kokari, amma za a kara mishi aiki saboda ina tare da sabon DPO wanda za a yi wa bayani kuma ya fara aiki tare da ku.

"Sabon DPO din zai turomin jerin sunayen duk yan sandan Igando, kuma zan tabbatar da wadanda sukayi shekara 3 suna aiki a nan domin canza su.

Edgal yace akwai bukatar binciko maboyar bata garin

An kuma kai sababbin ababen hawa na sintiri da kuma wayoyin sadarwar gaggawa guda 4.

Duk wanda aka kama a yankin da daddare dauke da makami to za a kama shi. Na kuma umarci yarana da su gwada wa ko waye karfin kayan aikin su matukar ya nemi karya doka. Inji Edgal.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel