2019: ‘Yan R-APC na iya kawowa Jam’iyyar tasgaro

2019: ‘Yan R-APC na iya kawowa Jam’iyyar tasgaro

- ‘Yan bangaren R-APC su na cigaba da karfi a Najeriya

- Wasu manyan ‘Yan APC ne su ka balle su ka kafa R-APC

- Daga cikin R-APC akwai Sanatoci da wasu ‘Yan Majalisu

Mun fahimci cewa ‘Yan Tawaren Jam’iyyar APC watau R-APC na kara karfi a kasar nan. Kwanakin baya ne dai wasu ‘Yan siyasa ‘Yan APC su ka bangare su ka kafa R-APC har ta kai aka shigar da su Kotu.

2019: ‘Yan R-APC na iya kawowa Jam’iyyar tasgaro

Shugaban ‘Yan R-APC na Kasa Injiniya Buba Galadima

Kwanakin baya mu ka samu labari cewa an kafa ofisoshin R-APC a kowane bangare na Jihar Kano. Tsohon Gwamnan Kano wanda kuma shi ne Shugaban Kwankwasiyya a kasar watau Rabiu Musa Kwankwaso yana tare da RAPC.

Akwai wasu ‘Yan Majalisa musamman daga Arewacin Kasar nan da su bangare daga APC su ka kafa RAPC. Kwanakin daya daga cikin ‘Yan Majalisun da ke bayan RAPC Hon. Nasiru Sule Garo ya nuna cewa ba su tare da Jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Wani Gwamna a Arewacin Najeriya ya bar Jam'iyyar APC

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshimhole yayi kokarin ganawa da tsohon Gwamnan kuma Sanata a yanzu Rabiu Musa Kwankwaso domin ganin bai ja Magoya bayan sa sun bar APC ba. Har yanzu dai ba a san yadda aka kare ba.

Kwanaki kun ji labari cewa ‘Yan bangaren R-APC wadanda su ka bangare daga Jam’iyyar APC mai mulki sun nada shugabannin su a kowace Jiha da bangare na kasar. Injiniya Buba Galadimane Shugaban ‘Yan tawaren na bangaren R-APC.

Kwanaki kun ji cewa kokarin da ake yi na kawo rabuwar kai a Jam’iyyar APC mai mulki ba zai kai ko ina ba. A 2014 dai ‘Yan nPDP su na cikin wadanda su ka kawowa Jm’iyyar PDP matsala a zaben 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel