Da duminsa: Buhari ya umarci wasu ministocinsa 2 su fara kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Rasha

Da duminsa: Buhari ya umarci wasu ministocinsa 2 su fara kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Rasha

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin kwaso ‘yan Najeriya da suka je kasar Rasha kallon wasan gasar cin kofin kwallon kafa na duniya amma guzurinsu ya kare.

Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya sanar da hakan a yau, Litinin, 16 ga watan Yuli.

Akwai rahotanni cewar ‘yan Najeriya da dama da suka je kasar Rasha kallon gasar cin kofin na duniya sun gaza dawowa, duk da an dade da cire Najeriya, saboda guzurinsu ya kare.

Da duminsa: Buhari ya umarci wasu ministocinsa 2 su fara kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Rasha

‘Yan Najeriya da suka makale a kasar Rasha

Garba Shehu ya bayyana cewar, shugaba Buhari ya umarci ministan harkokin kasashen waje, Garba Shehu, da ministan harkar jiragen sama, Hadi Sirika, su fara dawo da dukkan ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Rasha saboda karewar guzuri.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari na cigaba da burge duniya a taron da yake halarta a kasar holland

A jiya, Lahadi, ne aka kammala gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da kasar ta Rasha ta kasance mai kasance mai masaukin baki.

Kasar Faransa ta zama zakara bayan ta lallasa kasar Croatia da ci 4 - 2 a wasan zagayen karshe da aka buga jiya da rana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel