Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da Firam ministan kasar Netherland

Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da Firam ministan kasar Netherland

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya gana Firam Ministan kasar Netherlands, Markr Rutte, da yammacin yau a Hague, hedkwatar babban kotun duniya.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa ya tattauna da firam ministan ne al'amuran da suka shafi tattalin arziki, tsaro, da halin mutanen da suka rasa muhallansu a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Ya kara da cewa kasar Netherlands za ta cigaba da zama abokiyar hulda da mai muhimmanci da Najeriya.

A jawabin da ya saki, Buhari yace: " Na gana da firam minista Mark Rutte da yamman nan a Hague. Tattaunawanmu ya shafi abubuwa wanda ya kunshi tattalin arziki, harkokin tsaro da rayuwar yan gudun hijra a Arewa maso gabas."

Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da Firam ministan kasar Netherland

Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da Firam ministan kasar Netherland

KU KARANTA: Maryam Booth ta jinjinawa Sojojin Najeriya a wani yanayi mai burgewa

A jiya, Lahadi, ne shugaba Buhari ya bar Najeriya domin halartar wani taro a birnin Hague na kasar Holland inda zai gabatar da jawabi, kamar yadda kakakinsa, Garba Shehu, ya sanar tun ranar Asabar.

Bayan ya gabatar da jawabin, shugaba Buhari ya gana da wakilan kamfanin Heineken da Shell, da dukkansu keda reshe a Najeriya. Kazalika, shugaba Buhari ya gana da wasu ‘yan Najeriya dake zaune a kasar ta Holland.

Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da Firam ministan kasar Netherland

Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da Firam ministan kasar Netherland

Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da Firam ministan kasar Netherland

Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya gana da Firam ministan kasar Netherland

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel